Avalanche Ta Kashe Mutane Takwas a Tsaunukan California

 Jami’an tsaro sun tabbatar da cewa mutane takwas sun mutu sakamakon zubar dusar ƙanƙara (avalanche) a tsaunukan jihar California ta ƙasar United States.

avalanche

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a wani yankin tsaunuka da ake yawan zuwa yawon shakatawa, inda dusar ƙanƙara mai yawa ta gangaro ta rufe mutane da dama. Kungiyoyin ceto sun garzaya wurin domin tono wadanda abin ya rutsa da su, amma an tabbatar da mutuwar wasu daga cikinsu a wurin.

Hukumomi sun gargadi masu yawon bude ido da masu hawa tsaunuka da su yi taka-tsantsan a lokacin hunturu, domin sauyin yanayi da taruwar dusar ƙanƙara na iya haddasa irin wannan hatsari ba tare da gargadi ba.

Masana yanayi sun ce irin waɗannan avalanches na yawan faruwa idan dusar ƙanƙara ta yi yawa ko ta yi sanyi mai tsanani, wanda ke sa ƙasar dusar ta zame gaba ɗaya, ta zama barazana ga rayuka da dukiyoyi.

Post a Comment

Previous Post Next Post