Asali Aƙidar Masussuka da sauran ƴan Tatsine ita ce; ba su yarda da komai ba sai Alƙur’ani zalla. Shi ya sa za ka ga shafukansu a Facebook da sunan “Da’awar Alkur’ani Zalla".
Ma’ana; duk abin da ba Alkur’ani ba ne to sunansa “Ƙala-ƙato”, wato magana ce da ƙaton banza ya faɗa. Don haka ba su yarda da ita ba.
Saboda da ma Aƙidarsu Aƙida ce ta Khawarijawa. Su kuma
Khawarijawa asali Alƙur’ani kaɗai suka yarda da shi, suka yi watsi da Sunna, da
fahimtar Sahabbai da fassararsu ga Alƙur’ani. Shi ya sa suka rinƙa ɗaukar
Ayoyin Alƙur’ani, waɗanda suka sauka a kan kafirai - ba tare da ilimi da
fahimta ba - suka rinƙa ɗora su a kan Musulmai. Suka kafirta Musulmai, suka
halasta jinanensu.
To Masussuka da ya ga cewa; an fara yunƙurin ritsa shi, sai ya
fara kame - kame, sai ya fara neman taimakon Sufaye, sai yake ce musu: Shi yana
da matsala ne da Hadisai nau’i uku:
1- Hadisan da suka saɓa wa Alƙur’ani. (Don ya yaudari Sufaye).
2- Hadisan da suke koyar da ta’@ddanci. (Don ya yaudari
Gomnati).
3- Hadisan da suke taɓa darajar Annabi (saw). (Don ya yaudari
Sufaye).
To ka ga wannar dabara ce ta maras dabara.
To jin haka sai Sufaye ma suka ɗauka, suka ce: su ma ba su
yarda da irin waɗancan Hadisai ba.
Suke cewa; Hadisan makomar Iyayen Annabi (saw) sun saɓa
Alƙur’ani.
Sai Hadisai masu koyar da ta’@ddanci.
Sai kuma Hadisai masu taɓa darajar Annabi (saw). Don haka duka
ba su yarda da su ba.
Ai kwanaki an ji yadda Prof. Maqari ya yi irin wannar magana.
To da ma ba mamaki don Sufaye ma sun biye wa Masussuka a kan
inkarin sashen Hadisai. Da ma ƙin Hadisai shi ne babbar lema da ta haɗa dukkan
ƴan Bidi’a da mabiya son zuciya.
Amma asali shi Masussuka bai yarda da kowane Hadisi ba, saboda
shi ɗan tatsine ne, mai da’awar cewa; Hadisi maganar ƙaton banza ne.
To amma, ban da renin hankali na maras kunya mai son zuciya ba,
ai in dai wannar ƙa’idar za a bi, to shi ma Alƙur’ani sai ku fito ku ce: ba ku
yarda da Ayoyi nau’i uku ba:
1- Ayoyin da suka saɓa ma wasu Ayoyin Alƙur’ani.
2- Ayoyin da suke koyar da ta’@ddanci.
3- Ayoyin da suke taɓa darajar Annabi (saw).
- Saboda a cikin Alƙur’ani akwai Ayoyi da yawa da ake ganin
suna cin karo da juna.
- Haka akwai Ayoyin Jih@di, waɗanda Allah yake umurni da a yaƙi
kafirai, a k@she su, Ayoyi ne suna nan masu yawa a cikin Alƙur’ani.
Misali: Allah ya ce:
{فَإِذَا
انْسَلَخَ الْأَشْهُرُ الْحُرُمُ فَاقْتُلُوا الْمُشْرِكِينَ حَيْثُ
وَجَدْتُمُوهُمْ وَخُذُوهُمْ وَاحْصُرُوهُمْ وَاقْعُدُوا لَهُمْ كُلَّ مَرْصَدٍ
فَإِنْ تَابُوا وَأَقَامُوا الصَّلَاةَ وَآتَوُا الزَّكَاةَ فَخَلُّوا سَبِيلَهُمْ
إِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَحِيمٌ} [التوبة: 5]
Ya ce:
{قَاتِلُوا
الَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَلَا بِالْيَوْمِ الْآخِرِ وَلَا
يُحَرِّمُونَ مَا حَرَّمَ اللَّهُ وَرَسُولُهُ وَلَا يَدِينُونَ دِينَ الْحَقِّ
مِنَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ حَتَّى يُعْطُوا الْجِزْيَةَ عَنْ يَدٍ وَهُمْ
صَاغِرُونَ} [التوبة: 29]
Kowa ya san akwai Ayoyi masu yawa a maganar Jih@di.
- Haka kuma akwai Ayoyi da yawa da Allah ya zargi Annabi (saw)
a kan abubuwa daban - daban.
Misali: Allah ya ce:
{إِنَّا
أَنْزَلْنَا إِلَيْكَ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ لِتَحْكُمَ بَيْنَ النَّاسِ بِمَا
أَرَاكَ اللَّهُ وَلَا تَكُنْ لِلْخَائِنِينَ خَصِيمًا (105) وَاسْتَغْفِرِ
اللَّهَ إِنَّ اللَّهَ كَانَ غَفُورًا رَحِيمًا (106) وَلَا تُجَادِلْ عَنِ
الَّذِينَ يَخْتَانُونَ أَنْفُسَهُمْ إِنَّ اللَّهَ لَا يُحِبُّ مَنْ كَانَ
خَوَّانًا أَثِيمًا (107)} [النساء: 105 - 107]
Ya ce:
{عَفَا
اللَّهُ عَنْكَ لِمَ أَذِنْتَ لَهُمْ حَتَّى يَتَبَيَّنَ لَكَ الَّذِينَ صَدَقُوا
وَتَعْلَمَ الْكَاذِبِينَ (43)} [التوبة: 43]
Ya ce:
{مَا
كَانَ لِنَبِيٍّ أَنْ يَكُونَ لَهُ أَسْرَى حَتَّى يُثْخِنَ فِي الْأَرْضِ
تُرِيدُونَ عَرَضَ الدُّنْيَا وَاللَّهُ يُرِيدُ الْآخِرَةَ وَاللَّهُ عَزِيزٌ
حَكِيمٌ (67) لَوْلَا كِتَابٌ مِنَ اللَّهِ سَبَقَ لَمَسَّكُمْ فِيمَا أَخَذْتُمْ
عَذَابٌ عَظِيمٌ (68)} [الأنفال: 67، 68]
Ya ce:
﴿وَإِذۡ
تَقُولُ لِلَّذِیۤ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَیۡهِ وَأَنۡعَمۡتَ عَلَیۡهِ أَمۡسِكۡ عَلَیۡكَ
زَوۡجَكَ وَٱتَّقِ ٱللَّهَ وَتُخۡفِی فِی نَفۡسِكَ مَا ٱللَّهُ مُبۡدِیهِ
وَتَخۡشَى ٱلنَّاسَ وَٱللَّهُ أَحَقُّ أَن تَخۡشَىٰهُۖ﴾ [الأحزاب ٣٧]
Ya ce:
{يَاأَيُّهَا
النَّبِيُّ لِمَ تُحَرِّمُ مَا أَحَلَّ اللَّهُ لَكَ تَبْتَغِي مَرْضَاتَ
أَزْوَاجِكَ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَحِيمٌ} [التحريم: 1]
Ya ce:
{عَبَسَ
وَتَوَلَّى (1) أَنْ جَاءَهُ الْأَعْمَى (2) وَمَا يُدْرِيكَ لَعَلَّهُ يَزَّكَّى
(3) أَوْ يَذَّكَّرُ فَتَنْفَعَهُ الذِّكْرَى (4) أَمَّا مَنِ اسْتَغْنَى (5)
فَأَنْتَ لَهُ تَصَدَّى (6) وَمَا عَلَيْكَ أَلَّا يَزَّكَّى (7) وَأَمَّا مَنْ
جَاءَكَ يَسْعَى (8) وَهُوَ يَخْشَى (9) فَأَنْتَ عَنْهُ تَلَهَّى (10)} [عبس: 1 -
10]
Don haka, idan da gaske ne, to dole Masussuka, da sauran Sufaye
da suke cewa; ba su yarda da Hadisai masu kaza da kaza ba, to dole su zubar da
Ayoyin Alƙur’ani ma, waɗanda suka ci karo da juna, ko a cikinsu akwai koyar da
ta’@ddanci, ko akwai zargin Annabi (saw) da taɓa darajarsa (saw).
Saboda haka, da wannan za ka san cewa; abin nasu ba komai ba ne
face son zuciya da renin hankali kawai.
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani