Yau Amorim Yake Buga Wasa Na 50

Yau Asabar ƙungiyar Manchester United za ta fafata wasanta na 50 ƙarƙashin jagorancin mai horaswa Ruben Amorim tun bayan da ya koma ƙungiyar daga ƙungiyar Sporting CP ta Portugal a tsakiyar kakar wasanni ta bara, wanda ƙungiyar ta United ta ƙare a na 15 karo na farko a rayuwarta.
Yau zai buga wasa da Sunderland waɗanda suke a matakin na 6 yayin da ƙungiyar jajayen aljanun suke na 14 a teburin na Premier League.
A bayan nan an jiyo mai ƙungiyar James Ratcliffe ya bayyana cewa za su ba wa mai horaswar cikakkiyar dama har zuwa ƙarshen wannan kakar wasan. Duk da an jiyo masu ruwa da tsaki na kungiyar suna kiran mai horaswar da ya sauya zubin 'yan wasansa zuwa 433.
Kuna ganin ƙungiyar Red Devils ɗin za ta iya kai bantenta?

Post a Comment

Previous Post Next Post