Gary Lineker Ya Yi Amai Ya Lashe Abinsa


Tsohon ɗan ƙwallon gaba na Ingila wanda yanzu yana cikin masu bayar da rahoto akan wasanni ya yi amai ya lashe abin sa.
Lineker ya taɓa cewa, duk surutu da ake yi na ƙwarewar ɗan ƙwallon gaban Nijeriya wanda yake buga wa ƙungiyar Galatasaray ƙwallo Victor Osimhen ana nemansa sama ko ƙasa a rasa a babban wasa.
Gary ya fito ya ƙaryata kansa tare da bayar da haƙuri ga Osimhen bayan ganin irin rawar da ya taka a wasansa na Champions league da suka fafata da ƙungiyar Liverpool da take a Ingila. Wanda a wasan Victor ya zura ƙwallo ɗaya, kuma shi ne ya zamo ɗan wasan da ya fi kowane ɗan wasa ƙoƙari (Man If The Match).
Bayan an tashi wasan ne ya ce, lallai yadda na zaci Osimhen ashe ba haka yake ba, a wannan wasan ya bayyana asalin wane ne shi, don haka ina bayar da haƙuri a kan kalamaina sa suka gabata.

Post a Comment

Previous Post Next Post