Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump tare da wasu abokan tafiyar MAGA sun shiga cikin yaɗa bayanan ƙarya da ruɗani dangane da kisan Pretti, lamarin da ya tayar da ƙarin ce-ce-ku-ce a kafafen yaɗa labarai da na siyasa.
Bayan faruwar kisan, wasu manyan mutane da ke goyon bayan MAGA sun fara wallafa bayanai a shafukan sada zumunta, suna canja labarin abin da ya faru ko kuma suna jingina laifin ga wasu ba tare da hujja ba. Wadannan bayanai sun yi karo da rahotannin hukumomin tsaro da shaidun da aka tattara daga bincike.
Masana harkar watsa labarai sun ce irin wannan mataki na yada labaran ƙarya na iya rikitar da jama’a, tare da kawo cikas ga adalci da binciken gaskiya. Sun kara da cewa amfani da manyan dandamali wajen yada bayanan da ba su tabbata ba na kara rura wutar rabuwar kai a cikin al’umma.
Iyalan Pretti da masu fafutukar kare hakkin dan Adam sun yi Allah-wadai da abin da suka kira siyasantar da mutuwar wani dan Adam, suna kira ga shugabanni da ‘yan siyasa da su nuna gaskiya da kula da kalamansu, musamman a lokutan da ake bukatar tausayi da adalci.
Wannan lamari ya sake tayar da muhawara a Amurka kan rawar da shugabanni ke takawa wajen yaki da ko kuma yada labaran karya, da kuma yadda hakan ke shafar fahimtar jama’a game da manyan lamuran da suka shafi rayuka da tsaro.