Gobara ta Tashi a Ofishin hukumar ƴan gudun hijirar Falasɗinawa a gaɓar yamma ya kama da wuta

Hukumar kula da 'yan gudun hijirar Falasdinawa ta ce ginin shalkwatarta da ke Gabar yamma da kogin Jordan da aka fara rushewa yanzu yakama da wuta.

A makon daya gabata ne mahukuntan Isra'ila suka lalata wanu ɓangare na ginin hukumar.

Cikin wata sanarwa da ya sanya a shafinsa na X, shugaban hukumar Philippe Lazzarini,ya ce wutar da aka sanyawa ginin na su a yanzu shi ne hari na baya bayan nan da aka kai musu a wani yunƙuri na tarwatsa hukumar.

Ba dai a bayar da cikakken bayani akan yadda wutar ta tashi a ofoshin hukumar ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post