Hukumomi a jihar Zamfara, mai fama da matsalar tsaro a arewa maso yammacin Najeriya sun tabbatar da sace mutane 26 a wasu hare-hare da ƴan bindiga suka kai kan ƙauyuka biyu na ƙaramar hukumar Talatar Mafara a ƙarshen mako.
Talatar Mafara na daga cikin ƙananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaro a jihar, inda a shekarar 2021 ƴan bindiga suka sace ɗaliban makarantar mata ta Jangebe, kimanin 300.A tattaunawa da BBC, shugaban ƙaramar hukumar Talatar Mafara Yahaya Yari Abubakar ya ce ƴan bindigar sun kai hare-hare biyu a cikin ƙarshen mako.
"Shekaran jiya an shiga wani ƙauye mai suna Matuna, inda suka ɗauki mutum uku suka kuma kashe mutum ɗaya," a cewar Yari Abubakar.
Ya ƙara da cewa "sai suka sake dawowa suka sake kai hari a wani ƙauye da ake ce wa Tashar Kuturu, suka ɗauki mutum 23 kuma suka harbi wani mutum a hannu da kafa, mun kai shi asibitin cikin garin Jangebe ana nema masa lafiya."
A ranar Litinin ne rahotanni suka ɓulla kan cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari tare da sace mutane da dama waɗanda aba a ƙididdige yawansu ba.
A baya-bayan nan ƴan bindiga sun matsa ƙaimi wajen kai hare-hare a jihohin arewa maso yammacin Najeriya, inda suka kashewa da kuma sace mutane domin karɓar kuɗin fansa.
A makon da ya gabata wasu ƴan bindiga sun kai hari a Kajuru da ke jihar Kaduna inda suka sace masu ibada kimanin 170 a ƙauyen Kurmin Wali, inda duk da cewa wasu sun tsero, amma har yanzu akwai mutum 160 wadanda ba a san halin da suke ciki ba.
Haka nan a baya-bayan nan mahara sun kai hari a Makarantar Sakandiren Ƴanmata da ke garin Maga a jihar Kebbi, inda suka kashe mai gadi da sace ɗalibai 25.
Jim kaɗan bayan haka wasu ƴan bindigan sun kai hari a wata makaranta da ke ƙauyen Papiri a jihar Neja inda suka sace ɗalibai da malamai kusan 200.
Hukumomi a Najeriya na cewa suna ƙoƙari wajen magance matsalar, sai dai har yanzu ƴan bindigar na ci gaba da kai irin wadannan hare-hare waɗanda ke janyo salwantar rayuka da dukiya.
Lamarin ya haifar da durkushewar ayyukan tattalin arziki a yankin, inda manoma da dama ke gudun hijira, wasu kuma ba su iya noma kamar yadda suka saba yi a baya.