Ƙasar Iran ta sanar da naɗa Mojtaba Khamenei a matsayin sabon Jagoran Ƙoli na ƙasar bayan kashe mahaifinsa, tsohon jagoran ƙasar Ali Khamenei, a hare-haren sama da suka faru yayin rikicin da ke gudana a yankin.
An ce majalisar malamai ta ƙasar mai suna Assembly of Experts, wadda ke da alhakin zaɓen Jagoran Ƙoli, ita ce ta amince da naɗin Mojtaba bayan wani zama na musamman da ta gudanar.
Mojtaba Khamenei, wanda malamin addini ne mai shekaru kusan 56, ya dade yana da tasiri a cikin tsarin mulkin Iran duk da cewa bai taɓa rike wani babban mukamin gwamnati da aka zaɓa ba. Ana kuma ganin yana da kusanci da rundunar Islamic Revolutionary Guard Corps, daya daga cikin manyan rundunonin tsaron Iran.
Nadin nasa ya haifar da muhawara a cikin gida da wajen ƙasar, domin wannan shi ne karo na farko da ake ganin jagoranci a Iran ya wuce daga uba zuwa ɗa tun bayan Iranian Revolution na shekarar 1979.
Sauyin jagorancin ya zo ne a daidai lokacin da rikici ke ƙara tsananta a Gabas ta Tsakiya, inda ake ci gaba da tashin hankali tsakanin Iran, United States da kuma Israel.