Guinea Ta Rushe Manyan Jam’iyyun Adawa, Ta Mayar Da Kasar ‘Jam'iyya Daya’

 Gwamnatin Guinea ta rushe manyan jam’iyyun adawa na ƙasar, tana mai cewa duk wani ƙoƙari na siyasa zai kasance ƙarƙashin jam’iyyar gwamnati ɗaya, wanda ke haifar da tsarin “one‑party state.”

Guinea

Rahotanni sun ce wannan mataki na zuwa ne bayan tsananin rikice-rikice na siyasa da aka sha fama da su a baya-bayan nan, inda gwamnati ke zargin jam’iyyun adawa da shirya fitina da jefa ƙasar cikin tashin hankali.

Hukumar zabe ta ƙasar kuma ta dakatar da duk wani zaɓe da jam’iyyun adawa za su iya shiga, wanda hakan ya haifar da cece-kuce daga masu rajin dimokiradiyya a ƙasa da kuma ƙasashen duniya.

Masu sukar gwamnati sun bayyana wannan mataki a matsayin tacewar siyasa da ke kawar da yancin gudanar da jam’iyya a ƙasar, kuma suna ganin hakan na iya rage sahihancin tsarin dimokiradiyya a Guinea.

Gwamnatin ta ce tsarin “jam’iyya ɗaya” zai taimaka wajen tabbatar da tsaro, haɗin kai da zaman lafiya a cikin ƙasar, duk da cewa masu sharhi na cikin gida da na waje sun yi gargaɗi cewa hakan na iya haifar da ƙarin rikici.

Post a Comment

Previous Post Next Post