Jirgin Yakin Rundunar Sojojin Saman Biyafara A-26 Invader (B-26) Wanda Aka Taba Amfani Da Shi Wajen Kai wa Birnin Kano Hari.
Sojojin saman Biafra sun yi amfani da jirgin Douglas A-26 Invader (B-26) guda biyu lokacin yakin basasar Najeriya a 1967. An sayo wadannan jiragen masu lugudan bama-bamai da kuma amfani da su wajen kai hare-haren bama-bamai a kasa. Masu fafutukar kafa kasar Biafra sun nemi samun karin jiragen sama da suka hada da B-25 da C-47, domin fadada karfin su. An yi wa B-26 fentin launin toka kuma matukan jirgi kamar Jan Zumbach, wanda aka fi sani da "John Brown," wanda sojan haya ne, shine ya jagoranci kai hare-haren a kan dakarun Najeriya, ciki har da kai wa filin jirgin saman Kano hari a ranar lahadi 13 ga watan Agustan 1967. Biyo bayan wannan harin yasa sojojin USSR (Rasha) su ka fara jigilar jiragen yaki kirar MiG-17 na farko daga Masar zuwa Kano.
Masu fafutukar kafa kasar Biafra sun samu jirgin B-26 guda biyu, daya daga wani kamfanin binciken jiragen sama na farar hula da kuma wani mai yiwuwa daga kasar Cuba dauke da rajistar Amurka. Jiragen na B-26 an ajiye su a Enugu, su na sauka tayar daya jirgin ta fashe, kuma sun yi ta zirga-zirga, ciki har da kai hare-haren bama-bamai a kan wuraren Najeriya.
A daya hannun kuma, rundunar sojin saman Najeriya ta kai hare-hare ta sama a fadin kasar Biafra, da suka hada da auna muhimman ababen more rayuwa da cibiyoyin soji.
