Manyan Alamomin Ciwon Zuciya

Amfanin zuciya a jikin ɗan'adam shi ne jigilar jini mai ɗauke da iskar oxygen da abinci mai gina jiki zuwa dukkan sassan jiki, da kuma kwashe sharar jiki kamar carbon dioxide. Zuciya tana aiki kamar famfo mai ci gaba da bugawa, tana tabbatar da cewa kowane tantanin halitta ya sami isashshen abinci da oxygen don yin aikin yau da kullun. Idan zuciya ta daina aiki, jiki ba zai sami iskar oxygen ba, kuma sassan jiki zasu fara lalacewa cikin 'yan mintuna. A takaice, zuciya ita ce tushen rayuwa ta hanyar kula da zagayowar jini.

Zuciya

Masana lafiya sun bayyana cewa cutar zuciya ba kullum take farawa da ciwon kirji ba. A wasu lokuta tana farawa ne da gajiya mara dalili, musamman idan zuciya ta fara rasa ƙarfi wajen tura jini yadda ya kamata. Masana sun nuna cewa irin wannan gajiya na iya zama alamar farko ta matsalar zuciya.

Yadda Gajiya Ke Nuna Matsalar Zuciya

✔️ Gajiya ba tare da aiki ba

Idan kana jin kasala ko gajiya duk rana ba tare da wani aiki mai nauyi ba, zuciya na iya kasa kai isasshen jini ga jiki.

✔️ Gajiya yayin tafiya kaɗan

Idan kana gajiya ko numfashi na wahala bayan ɗan tafiya kaɗan, hakan na iya nuna zuciya na wahala.

✔️ Gajiya da jiri ko suma

Idan gajiya tare da jiri ko duhun gani, yana iya nuna jini ba ya isa kwakwalwa yadda ya kamata.

✔️ Gajiya tare da kumburin ƙafa

Wannan na iya faruwa idan zuciya ta kasa fitar da jini yadda ya kamata, ruwa ya fara taruwa a jiki.

✔️ Gajiya da wahalar numfashi yayin bacci

Idan kana jin kamar kana wahalar numfashi idan ka kwanta, na iya zama alamar matsalar zuciya.

 Abin Da Ya Kamata Ka Ya

~ Idan gajiya ta zama kullum kuma ba ka san dalili ba, a je asibiti

~ A duba hawan jini, suga da cholesterol

~ A rage gishiri, mai da abinci mai kitse

~ A motsa jiki lokoci bayan lokoci 

~ A daina Shan taba sigari da barasa

Post a Comment

Previous Post Next Post