Gwamnatin Mexico da Hukumar Leken Asiri ta Amurka (CIA) sun yi watsi da wani rahoto da ke cewa jami’an CIA sun shiga kai tsaye cikin hare-haren kashe mambobin ƙungiyoyin miyagun ƙwayoyi a Mexico.
Rahoton, wanda kafar CNN ta wallafa, ya yi zargin cewa CIA ta ƙara yawan ayyukan sirri a Mexico, inda ake cewa jami’anta sun taimaka ko ma suka shiga kai tsaye wajen kai hare-haren da suka yi sanadin mutuwar wasu ‘yan ƙungiyoyin safarar miyagun ƙwayoyi.
Sai dai Ministan Tsaron Mexico, Omar Garcia Harfuch, ya bayyana cewa gwamnatin ƙasar ba za ta amince da duk wani aiki na sirri ko farmaki daga wata ƙasa a cikin ƙasar Mexico ba tare da izininta ba. Ya ce rahotannin da ke nuna cewa ƙasashen waje na gudanar da hare-hare a Mexico ba gaskiya ba ne.
Hukumar CIA ma ta fitar da sanarwa inda ta kira rahoton da cewa “ƙarya ce mai haɗari,” tana mai cewa irin waɗannan rahotanni na iya taimakawa ƙungiyoyin masu safarar miyagun ƙwayoyi wajen yaɗa farfaganda da kuma jefa rayuwar jami’an Amurka cikin haɗari.
Rahoton CNN ya yi ikirarin cewa wasu ayyukan CIA sun haɗa da harin mota da ya kashe wani da ake zargin ɗan ƙungiyar Sinaloa Cartel ne mai suna Francisco Beltran, wanda aka fi sani da “El Payin.” An ce harin wani ɓangare ne na sabon kamfen na sirri da ake yi domin murƙushe ƙungiyoyin miyagun ƙwayoyi a Mexico.
Lamarin ya sake tayar da muhawara kan rawar da Amurka ke takawa a yaƙin da Mexico ke yi da ƙungiyoyin miyagun ƙwayoyi, musamman bayan rahotannin baya-bayan nan da suka nuna cewa jami’an Amurka sun shiga wasu ayyukan haɗin gwiwa a yankunan kan iyaka.