Najeriya Ta Sake Gaza Cimma Adadin Haƙon Mai da OPEC Ta Gindaya

Najeriya ta sake kasa cimma adadin haƙon ɗanyen mai da Ƙungiyar Ƙasashe Masu Fitar da Mai ta Duniya (OPEC) ta ware mata, bayan da ta samar da matsakaicin ganga miliyan 1.49 a kowace rana a watan Afrilu, ƙasa da adadin ganga miliyan 1.5 da aka ɗora mata.

Alƙaluman da Hukumar Kula da Harkokin Mai ta Najeriya (NUPRC) ta fitar sun nuna cewa ƙasar ta samar da matsakaicin ganga 1,488,540 na ɗanyen mai a kullum a watan Afrilu, wanda ya kai kusan kashi 99 cikin 100 na adadin da OPEC ta ware mata. Idan aka haɗa da condensates, yawan man da aka samar a kullum ya kai ganga miliyan 1.66.

A watan da ya gabata, NUPRC ta bayyana cewa yawan haƙon mai ya kai matsakaicin ganga miliyan 1.8 a rana. Sai dai bayanan da aka fitar ranar Talata sun saɓa da wannan rahoto. Sabbin alkaluman sun nuna cewa Najeriya ta ci gaba da kasa kai wa adadin OPEC karo na tara a jere tun daga watan Yulin 2025.

Takardar bayanan NUPRC ta nuna cewa jimillar ɗanyen mai da condensates da aka samar ta kai kololuwa ganga miliyan 1.85 a rana a cikin watan, yayin da mafi ƙarancin yawan haƙon ya tsaya a ganga miliyan 1.46 a rana. Jaridar The PUNCH ta ruwaito cewa alkaluman watan Afrilu sun fi na watan Maris armashi, inda a wancan lokacin aka samar da ganga miliyan 1.55 a rana.

Shekaru da dama yanzu Najeriya na fama da matsalolin da suka haɗa da satar ɗanyen mai, lalata bututun mai, tsufan kayan aiki da ƙarancin saka hannun jari a ɓangaren haƙo mai. Duk da cewa an samu ɗan ƙarin yawan haƙo mai a watan Afrilu idan aka kwatanta da Maris, har yanzu bai isa ya kai adadin da OPEC ta gindaya ba, lamarin da ke nuna cewa har yanzu akwai manyan ƙalubale wajen ƙara yawan samar da mai duk da ƙoƙarin gwamnati.

Jaridar The PUNCH ta kuma ruwaito cewa yawan haƙon ɗanyen mai a watan Maris ya kai ganga miliyan 1.38 a rana. Duk da samun ƙarin ganga dubu 69 daga ganga miliyan 1.31 da aka samar a watan Fabrairu, har yanzu Najeriya na ƙasa da adadin OPEC da ganga dubu 117 a rana.

Post a Comment

Previous Post Next Post