Muhammadu Rumfa shi ne sarki na ishirin a jerin sarakunan Kano. Shi ne wanda aka yi wa sarautar Makaman Kano lokacin yana ɗan shekaru shida a duniya. Wannan kuwa ta faru ne bayan wani abin mamaki da ya faru da shi. Shi Muhammadu Rumfa asalin sunansa shi ne Muhammadu Mansur.
Sarkin musulmi Muhammadu Rumfa yana cikin Sarakunan Hausawa da suka mulki Kano, shi ne wanda ya taso da gidan Sarki daga kusa da dutsen Dala zuwa gidan Makama saboda cunkoson jama'a da aka fara samu a yankin a lokacin, da kuma yunkurinsa na samar da tsaro ga Sarki.
Sarki Rumfa ne ya gina gidan sarkin Kano na yanzu, kuma ya kawo sauye-sauye da dama a tsarin tafiyar da sarauta a Kano. A lokacin ne sarki ya fara zama kyam a kan karaga ba tare da yana motsi ba, kuma shi ne ya fara sunke, wato sarki ya yi amfani da gefen rawaninsa ya rufe bakinsa, don kar a ringa ganin lokacin da sarkin ya ke magana.
Muhammad Dan Yakubu wanda aka fi sani da Muhammad Rumfa shi ne Sarkin Kano daga shekarar 1463 zuwa 1499. Sarautarsa ta kasance da tarin dukiya da wadata wanda hakan ke nuni da yadda masarautar Sarkin Musulmi ta mamaye harkokin kasuwanci a yankin. Karkashin Jagorancin Shahararren Malamin Berber, Muhammad Al-Maghili, shi ma ya kawo ci gaban Musulunci a Kano.
A dunkule a tarihin Kano Muhammadu Rumfa ya kawo sanannun sauye-sauye goma sha biyu a mulkin da yayiwa Kano, wadanda suka hada da; fadada katangar birni, gina katafariyar fada, Gidan Rumfa, gina babban masallacin juma'a na cikin garin Kano, nada bayi a masarautu da kafa Kasuwar Kurmi.
Sauye-sauyen da Rumfa ya yi ya kuma tabbatar da cewa shi ne ginshikin da ya kai Kano ga kololuwar cigaban siyasarta.
Saboda shaharar sarkin musulmi Muhammad Rumfa, hatta sarakunan fulani zakaji anayi musu kirari da magajin Rumfa.
Rumfa ya gaji Sarauta a shekara ta 1463. Mulkinsa ya kasance da ci gaban tattalin arziki da ba a taba ganin irinsa ba, da gyare-gyaren gudanarwa da dama, da kuma ci gaban ababen more rayuwa. Rumfa ya bunkasa tattalin arziki wanda ya yi sanadiyar zuwan ‘yan kasuwa Kano, galibinsu Larabawa, Kanuri, Berber da Fula.
Yaki Da Katsina
Yakin da Rumfa ya yi da Katsina shi ne karo na farko da aka gwabza yaki tsakanin kasashen biyu. Ya yi shekara goma sha ɗaya ba tare da wata wanƙwaƙƙwaran nasara ba. A lokacin wannan yakin, an ce Sarkin Musulmi Muhammadu Rumfa shi ne sarki na farko a tarihi da ya yi amfani da “Dawakan Zagi.
Gado
Ana dai kallon Rumfa a matsayin babban sarkin Kano. Wasu daga cikin gine-ginen da ya gina da gyare-gyaren harkokin mulki a zamaninsa har yanzu ana amfani da su a Kano. Sunan fadar Sarki, Gidan Rumfa. Haka ita ma babbar kwalejin Rumfa ta Kano.
Shi mutumin kirki ne, adali kuma abin koyi. Ba zai iya samun wanda ya kai girmansa ba, tun daga lokacin da aka kafa Kano, har a nade kasa..tabbas babu Sarki da ya fi Rumfa shahara.
