Kwamandan hedikwatar rundunar juyin juya halin Iran ya bayyana cewa Iran ba za ta ci gaba da tattaunawa ba har sai an kawo ƙarshen yaƙi ta ko wanne fanni.
Mohammad Ali Jafari ya ce dole ne a fara cika wasu sharudda kafin komawa teburin tattaunawa, ciki har da ɗage takunkumi, sakin kuɗaɗen da aka ƙwace, da kuma biyan diyya kan barnar da yaƙi ya haifar. Ya kuma jaddada cewa dole ne a amince da ikon Iran kan mashigar Hormuz.
Ya ƙara da cewa shugaban Amurka ya shiga wani hali na rashin tabbas saboda gazawa wajen cimma manufofinsa, yana mai cewa ana ƙoƙarin maye gurbin nasarar da ba a samu a yaƙi da matakan diflomasiyya
