Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta ƙasa (NCDC) ta sanya biranen Legas da Tarayyar Abuja, da ma wasu jihohin ƙasar cikin shirin ko-ta-kwana, biyo bayan bullar wani sabon nau'in kwayar cutar Ebola mai hadarin gaske mai suna 'Bundibugyo' a sassa na Gabas da Tsakiyar Afirka.
A cikin wata sanarwar gaggawa ta kiwon lafiyar jama'a da hukumar ta aike wa kwamishinonin lafiya na jihohin kasar, ta yi gargaɗin cewa Najeriya na fuskantar babban barazanar shigowar wannan kwayar cuta. Hakan na faruwa ne sakamakon karuwar yaduwar cutar a yankunan da abin ya shafa, da zirga-zirgar jiragen sama na kasa da kasa, da kuma matsalar iyakokin kasa masu kofofin barayi da ke saukaka zirga-zirgar mutane.Sanarwar, mai kwanan wata 27 ga watan Mayun shekarar 2026, ta zo ne a daidai lokacin da fargaba ke karuwa game da yaduwar nau'in cutar ta 'Bundibugyo'—wani boyayyen nau'in Ebola wanda a halin yanzu ba shi da gamsaccen rigakafi ko kuma takamaiman magani da aka amince da shi.
Jihohin Da Ke Cikin Babban Hadari
Hukumar NCDC ta ware wasu takamaiman jihohi a matsayin masu fuskantar babban hadari saboda kasancewar manyan filayen jiragen sama na kasa da kasa, tashoshin jiragen ruwa, hanyoyin kan iyaka, da kuma yawan cinkoson jama'a. Jihohin sun hada da:
Legas
Babban Birnin Tarayya (FCT)
Rivers
Kano
Enugu
Borno
Akwa Ibom
Cross River
Taraba
Adamawa
"Manufar farko ta yunkurinmu na shirin ko-ta-kwana a matakin kasa ita ce tabbatar da cewa kowace jiha da kuma babban birnin tarayya (FCT) suna da cikakkiyar damar ganowa, killacewa, da kuma daukar matakin gaggawa a kan kowane mutum da ake zargi yana dauke da cutar. Wannan zai taimaka wajen kare ma'aikatan lafiya da kuma dorewar samar da muhimman ayyukan jiyya," in ji hukumar NCDC.