An samu Hanyoyin Yadda za a Warware Rikicin Lebanon

Kafar watsa labarai ta BBC ta ruwaito cewa ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce an samu gagarumin ci gaba wajen kawo ƙarshen rikicin Lebanon, wanda yake daga cikin manyan manufofin Iran a tattaunawar da ta yi da Amurka a Switzerland.

Ya bayyana cewa matakan da aka ɗauka a tattaunawar sun nuna yiwuwar samun ci gaba mai dorewa wajen dakatar da rikicin.

Ya ƙara da cewa gwajin farko na wannan nasara shi ne yadda sabuwar hanyar haɗin gwiwar “de-confliction cell” za ta fara aiki tsakanin Iran, Amurka da Lebanon domin tabbatar da tsagaita wuta da kauce wa sake barkewar rikici.

A halin da ake ciki, masu shiga tsakani daga ƙasashen Pakistan da Qatar sun tabbatar da cewa an kammala zagaye na farko na tattaunawar da ake yi a Switzerland tsakanin Amurka da Iran, inda suka ce an samu ci gaba mai ƙarfafawa.

Sun kuma bayyana cewa an tsara wata hanya da za ta kai ga cimma yarjejeniya ta ƙarshe cikin kwanaki 60 masu zuwa.

Sai dai duk da kammala wannan mataki na farko, an ce za a ci gaba da tattaunawar a cikin makon nan domin zurfafa tattaunawa kan batutuwan da suka rage.

A lokaci guda, Shugaban Lebanon, Joseph Aoun, ya fara tattaunawa da jami’an Amurka da Qatar kan yadda za a tabbatar ɗa dorewar tsagaita wuta da zaman lafiya a yankin.

Post a Comment

Previous Post Next Post