Farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya ci gaba da faduwa a ranar Juma'a, yayin da karin tankokin dakon mai suka fara fita daga mashigar ruwa ta Hormuz mai matuƙar muhimmanci, lamarin da ya rage fargabar katsewar samar da mai duk da wani hari da aka kai wa wani jirgin dakon kaya a Tekun Oman.Farashin danyen mai na Brent, wanda ake amfani da shi a matsayin ma'aunin farashin mai a duniya, ya ragu da kashi 4.34 cikin ɗari inda ya tsaya kan dala 71.99 kan kowace ganga ta kwangilar watan Agusta.
Haka kuma, farashin danyen mai na West Texas Intermediate (WTI) na Amurka ya sauka da kashi 3.74 cikin ɗari zuwa dala 69.23 kan kowace ganga. Wannan shi ne karon farko da farashin WTI ya rufe kasa da dala 70 tun ranar 27 ga Fabrairu, wato kwana guda kafin fara yakin Iran.
Saukar farashin ta zo ne yayin da masu zuba jari ke ci gaba da sa ido kan abubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, tare da tantance ko yunƙurin diflomasiyya na baya-bayan nan zai rage haɗarin tangardar samar da mai da sauran kayayyaki.
Wani jami'in gwamnatin Amurka ya shaida wa MS NOW cewa Iran ce ke da alhakin harin da aka kai wa wani jirgin dakon kaya a kusa da gabar Tekun Oman, cikin mashigar Hormuz. A cewar jaridar Wall Street Journal, jirgin yana tafiya ne ƙarƙashin tutar ƙasar Singapore.
Hukumar United Kingdom Maritime Trade Operations (UKMTO) ta ce jirgin ya ba da rahoton cewa babu wanda ya rasa ransa ko ya jikkata, sannan babu wata illa ga muhalli sakamakon harin.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya zargi Iran da karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta hanyar kai hare-haren jiragen marasa matuƙa (drones) a mashigar Hormuz.
Trump ya ce, "An yi barna, amma jirgin ya ci gaba da tafiyarsa. Mun harbo wasu jiragen sama marasa matuƙa guda uku. A bayyane yake wannan karya ce ta wauta ga yarjejeniyar tsagaita wutar da muka cimma."