Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta kama wasu tsofaffi biyu masu shekaru 84 da 75 a jihar Abia bisa zargin sayar da miyagun ƙwayoyi ga ɗaliban makarantun sakandare.
Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ya ce an kama Godwin Obiora mai shekara 75 a Umuahia bayan samun bayanan sirri cewa yana sayar da ƙwayoyi daga shagon sayar da magunguna. An kuma ƙwace kilogram 4.64 na ƙwayoyin tramadol da diazepam a wajensa.
Haka kuma an kama Godfrey Orji mai shekara 84 bayan jami’an tsaro suka kama shi a wata makarantar sakandare yana zargin ba wasu ɗalibai biyu ƙwayoyi. Wani ɗalibi mai shekara 15 ya shaida wa masu bincike cewa mutumin yana ba shi ƙwayoyi domin amfani da su da kuma sayar wa sauran ɗalibai.
NDLEA ta ce an sanya ɗaliban cikin shirye-shiryen ba su shawara da gyara hali, yayin da ake shirin gurfanar da mutanen biyu a kotu.
A wasu hare-haren da ta kai a faɗin ƙasar, hukumar ta kama wasu mutane da dama tare da ƙwace hodar iblis da tabar wiwi masu yawa a jihohin Lagos, Kogi, Ekiti da Oyo.
Shugaban NDLEA, Buba Marwa, ya yaba wa jami’an hukumar bisa nasarorin da suka samu, tare da buƙatar su ci gaba da yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi a faɗin ƙasar.
