OpenAI Ta Ƙaddamar da Guntun AI Na Farko 'Jalapeño' Domin Rage Farashi da Ƙarfafa Ayyukan ChatGPT


Kamfanin OpenAI ya sanar a ranar Laraba da ƙaddamar da guntun kwamfuta na farko da ya ƙera da kansa mai suna Jalapeño, a wani muhimmin mataki na faɗaɗa harkokinsa daga samar da kayayyakin amfani ga masu amfani zuwa zama babban mai samar da kayayyakin more rayuwa na basirar wucin gadi (AI infrastructure).

Kamfanin ya bayyana a cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa cewa an ƙera guntun ne tare da haɗin gwiwar kamfanin Broadcom domin gudanar da ayyukan lissafi cikin inganci ga ChatGPT da kuma wakilin rubuta lamba na OpenAI mai suna Codex. Haka kuma, an tsara shi ne domin ɗaukar nauyin sabbin ayyukan AI da kamfanin ke shirin haɓakawa nan gaba.

OpenAI ta ce duk da cewa har yanzu ana ci gaba da gwaje-gwajen tantance cikakken ƙarfinsa, sakamakon farko ya nuna cewa Jalapeño na samar da aiki mai inganci sosai idan aka kwatanta da yawan wutar lantarkin da yake amfani da ita, fiye da mafi ingancin guntayen AI da ake amfani da su a halin yanzu.

A bara ne OpenAI da Broadcom suka sanar da shirin haɗin gwiwa na ƙera guntayen AI na musamman da za su samar da ƙarfin lissafi da ya kai gigawatt 10. Sai dai a ranar Laraba ne suka bayyana guntun farko da aka samar daga wannan haɗin gwiwar.

Manyan kamfanonin fasaha irin su Google da Amazon ma sun fara ƙera nasu guntayen AI domin su daidaita aikin na'urorinsu da tsarin AI da suke haɓakawa, tare da rage dogaro da kamfanonin da ke ƙera guntu irin su Nvidia.

OpenAI ta ce Jalapeño ba guntu ne na amfani gaba ɗaya ba, illa an tsara shi musamman domin gudanar da ayyukan manyan tsarin fahimtar harshe na basirar wucin gadi (Large Language Models).

Babban shugaban binciken fasaha na kamfanin zuba jari na Quilter Cheviot, Ben Barringer, ya shaida wa CNN a watan Nuwamban bara cewa, babu wani babban kamfanin fasaha da ke son ci gaba da dogaro gaba ɗaya kan Nvidia.

Ya ce, "Kowa na ƙoƙarin faɗaɗa hanyoyin samar da guntayen AI domin rage dogaro da kamfani guda."

Sanarwar ƙaddamar da sabon guntun ta zo ne yayin da OpenAI ke shirye-shiryen gudanar da sayar da hannun jarinsa ga jama'a (IPO), wanda ake hasashen zai iya kai darajar kamfanin zuwa dala tiriliyan ɗaya.

Wannan na ƙara matsin lamba ga kamfanin wajen tabbatar da cewa zai iya samar da kuɗaɗen shiga da suka dace da wannan babban ƙima.

A halin yanzu, kasuwar kayayyakin more rayuwa na AI na samar da riba mai yawa. Kamfanin Nvidia ya zama mafi darajar kamfani a duniya ne saboda guntayensa da tsarin da ya ƙera sun zama ginshiƙan cibiyoyin bayanai (data centers) da ke tafiyar da manyan tsarin AI.

A lokaci guda kuma, kamfanonin AI na fafatawa wajen tabbatar da samun isasshen ƙarfin lissafi da makamashi domin gudanar da sabbin ayyukan AI masu rikitarwa, musamman waɗanda ke aiki a matsayin wakilai (AI agents) maimakon amsa tambayoyin masu amfani kawai.

OpenAI ta taɓa bayyana cewa akwai buƙatar gina manyan kayayyakin more rayuwa na AI domin rage kuɗaɗen gudanar da ayyukanta.

Ga masu amfani da fasaharta kuwa, OpenAI ta ce sabon guntun Jalapeño zai taimaka wajen rage kuɗin tafiyar da tsarin AI, wanda hakan zai sa ayyukanta su kasance masu araha tare da ƙara yawan mutanen da za su iya amfani da su.

Shugaban OpenAI kuma wanda ya kafa kamfanin tare, Greg Brockman, ya ce ƙera mafi yawan sassan fasahar kamfanin da kansa zai ba OpenAI damar samar da ƙarin ƙwarewar AI cikin inganci, tare da ci gaba da faɗaɗa damar amfani da fasahar ga al'umma baki ɗaya.

Post a Comment

Previous Post Next Post