Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Amurka za ta gana da Iran a birnin Doha na ƙasar Qatar ranar Talata, yayin da jami'an Amurka suka ce bangarorin biyu sun amince su dakatar da rikicin a halin yanzu tare da ci gaba da tattaunawar diflomasiyya bayan hare-haren da aka kai a ƙarshen mako.Sai dai Iran ba ta tabbatar da cewa za a gudanar da wannan ganawa ba, duk da ikirarin da Trump ya yi.
A wani bangare kuma, rikici ya ci gaba tsakanin ƙungiyar Hezbollah da Isra'ila a ƙasar Lebanon duk da wata yarjejeniya da aka cimma kwanan nan tsakanin bangarorin. Iran ta buƙaci Isra'ila ta janye duka sojojinta daga Lebanon a matsayin wani muhimmin sharadi na cimma yarjejeniya ta ƙarshe da Amurka.
Mashigin Hormuz
Bayanan sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa sun nuna cewa zirga-zirga ta ɗan ƙaru a cikin sa'o'i 36 da suka gabata ta mashigin Hormuz, wanda ke da matuƙar muhimmanci ga safarar danyen mai a duniya.
Haka kuma, ƙarin jiragen ruwa na amfani da hanyar da ke kusa da gabar tekun Oman domin kauce wa yankin, lamarin da masana ke ganin na iya rage tasirin barazanar da Tehran ke yi na rufe ko takaita amfani da mashigin Hormuz, duk da cewa Iran ta jaddada cewa har yanzu tana da ikon sarrafa mashigin.