Trump Ya Yaba wa FIFA Kan Soke Dakatarwar Balogun

Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yaba wa Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) bayan ta soke hukuncin dakatar da ɗan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon ƙafar Amurka, Folarin Balogun, sakamakon jan katin da aka nuna masa.
Kwamitin ladabtarwa na FIFA ya janye hukuncin dakatar da Balogun daga buga wasa ɗaya, wanda aka ɗora masa kai tsaye bayan an kore shi da jan kati a wasan zagaye na 32 da Amurka ta doke Bosnia da Herzegovinar.
Sakamakon wannan hukunci, Balogun zai samu damar taka leda a wasan zagaye na 16 na gasar cin Kofin Duniya ta FIFA, inda Amurka za ta kara da Belgium ranar Litinin.
Trump ya bayyana cewa matakin da FIFA ta ɗauka babban abin farin ciki ne ga tawagar ƙasar Amurka, yana mai cewa hakan zai ƙara wa ƙungiyar ƙarfin gwiwa gabanin wannan muhimmiyar fafatawar neman gurbin zuwa zagaye na gaba.

Post a Comment

Previous Post Next Post