An Sake Sanya Dokar Hana Hawan Babura A Kanan Hukumomin Katsina 19 Cikin 34

Gwamnatin Jihar Katsina ta  sake ƙaƙaba dokar haramta zirga-zirgar babura da Adaidaita Sahu da dare a ƙananan hukumomi 19 cikin 34 da ke cikin jihar.

Gwamnatin Jihar Katsina ta sake tabbatar da haramcin zirga-zirgar baburan haya da kuma adaidaita sahu da daddare a ƙananan hukumomi 19 na jihar, biyo bayan hukunce-hukuncen da aka gabatar da suka shafi, ɗauke service na tsawon mako guda da hana sana'ar POS da canjin waya da kuma hawan babur, a wani mataki na ƙarfafa tsaro da yaƙi da ayyukan 'yan bindiga.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan harkokin tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Hon. Alhaji Nasiru Mu'azu, ya fitar, ya bayyana cewa dokar za ta fara aiki daga ƙarfe 8:00 na dare zuwa 6:00 na safe. Sanarwar ta ce: "Wannan umarni ya shafi ƙananan hukumomin da matsalar 'yan bindiga da sauran laifuffuka masu alaƙa da rashin tsaro suka fi ƙamari."
Ƙananan hukumomin da dokar ta shafa sun haɗa da:Sabuwa da Ɗandume da Funtua da Faskari da Bakori da Ƙanƙara da Ɗanja da Ƙafur da Malumfashi da Musawa da Matazu Ɗan Musa da Safana da Dutsinma da Kurfi da Charanchi da Jibia da Batsari da kuma Kankia.

Sanarwar ta kuma jaddada cewa: "Ya kamata jama'a su fahimci cewa manufar wannan doka ita ce dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a waɗannan yankuna da matsalar tsaro ta addaba.

Post a Comment

Previous Post Next Post