Matasa Sun Gudanar Da Taron Goyon Bayan Tinubu Da Gwamnan Jihar Kwara

Dubban magoya bayan jam'iyyar APC sun gudanar da wani gangami a birnin Ilorin na Jihar Kwara domin nuna goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma ɗan takarar gwamnan jihar, Injiniya Salihu Yakubu Danladi, gabanin zaɓen 2027.

Matasa

Gangamin mai taken "Kwara APC Ndupe Rally", wanda ƙungiyar Kwara Progressives ta shirya, ya samu halartar magoya baya da jiga-jigan jam'iyyar daga yankunan sanatoci uku na jihar.

Masu gangamin sun yi tattaki ta manyan titunan Ilorin kafin su ƙare a sakatariyar APC ta jihar, inda suka bayyana goyon bayansu ga Tinubu da sauran 'yan takarar jam'iyyar.

Da yake zantawa da manema labarai, mai kula da ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors a Kwara, Abdullateef Gidado Alakawa, ya yabawa Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq kan jagorancinsa, tare da cewa yawan mutanen da suka halarci gangamin ya nuna irin amincewar da jama'a ke da ita ga APC da 'yan takararta.

Gangamin ya samu halartar ɗan takarar gwamnan APC, Injiniya Salihu Yakubu Danladi, da sauran 'yan takarar jam'iyyar, yayin da masu shirya taron suka ce yana daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa goyon bayan APC a faɗin jihar kafin babban zaɓen 2027.

Post a Comment

Previous Post Next Post