Hukumomi a jihar Kwara da ke arewa ta tsakiyar Najeriya sun rufe makarantu a ƙananan hukumomi biyar da ke jihar sakamakon ƙaruwar matsalolin tsaro a yankin.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan ilimi na jihar Lawal Olohungbebe ya fitar, ya ce hukumomin jihar sun ƙuduri aniyar daƙile ayyukan masu garkuwa da mutane.Wannan matakin na zuwa ne bayan wani hari da ƴan bindiga suka kai wani coci a jihar a ranar Talata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla masu ibada biyu, da sace gwammai.
Ya kuma ce za a ci gaba da kulle makarantun ne har sai an samu rahoton tabbacin tsaro cewa lammura sun koma kamar yadda suke.
Sanarwar ta ce an ɗauki matakin rufe makarantun ne a matsayin matakin tsaro na gaggawa, sakamakon yadda ake ganin ƴan bindiga na kai hari kan ɗalibai tare da sace su don neman kuɗin fansa.
Ko a ranar Litinin da ta gabata, an sace wasu ɗalibai fiye da ashirin a wata makarantar kwana da ke jihar Kebbi, lamarin da ke ƙara nuna ta'azzarar matsalolin tsaro a wasu sassan ƙasar.