Babban daraktan World Health Organization (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya nuna damuwa kan hare-haren da Israel ta kai kan cibiyoyin man fetur a Iran, yana mai gargaɗin cewa hakan na iya haifar da mummunar illa ga lafiyar jama’a da muhalli.
A wani saƙo da ya wallafa, shugaban WHO ya ce kai hari kan irin waɗannan muhimman cibiyoyi na iya janyo gurbatar iska, gobara mai yawa da matsalolin lafiya ga mutanen da ke zaune a yankunan da abin ya shafa.
Ya kuma jaddada cewa rikici da hare-haren soja kan manyan cibiyoyin samar da makamashi na iya kawo barazana ga lafiyar jama’a a yankin da ma duniya baki ɗaya, musamman idan ya jawo gurbacewar muhalli ko tangarda ga samar da muhimman kayayyaki.
Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi kira ga dukkan ɓangarorin da ke cikin rikicin su guji kai hari kan muhimman cibiyoyin farar hula, yana mai cewa kare rayuka da lafiyar jama’a ya kamata ya kasance a gaba.
Hare-haren na zuwa ne yayin da rikici tsakanin Israel da Iran ke ƙara tsananta, lamarin da ke haddasa fargaba game da tasirin sa ga yankin Gabas ta Tsakiya da kuma kasuwannin makamashi na duniya.