Gwamna jihar Zamfara Lawal Dauda ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP tare da komawa jam'iyyar APC mai mulki a matakin tarayya.
Gwamnan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Nuhu Salihu Anka ya fitar, inda ya ce ya yanke shawara ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki da magoya bayansa.Gwamna Lawal ya ƙara da cewa ya yi la'akari ne da irin rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam'iyyar PDP a matakin ƙasa da jiha, wanda a cewarsa ke haifar da ruɗani da kawo tsaiko wajen tafiyar da mulki a jihar.
Ya ce komawa APC za ta taimaka masa wajen haɗa ƙarfi da ƙarfe da gwamnatin tarayya domin tabbatar da tsaro da ci gaban jihar baki ɗaya.