Dabarun Yin Azumi a lokacin zafi

Duk da cewa a yankunan Afirka irin arewacin Najeriya da kudancin Jamhuriyar Nijar da kuma makwafta, an fara azumin Ramadana na 2026 cikin yanayi na ni'ima, lamarin ya sauya a baya-bayan nan, inda ake zabga zafi.

A hasashen da ta fitar na watan Maris, hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMet ta ce za a yi fama da zafi a fadin kasar.

Ta ce akasari yanayi zai kasance tsakanin digiri 30 zuwa 40 a ma'aunin yanayi na salshiyas, amma ana hasashen za a iya samun zafin da zai kai 38 zuwa 41 ma'aunin salshiyas a arewacin kasar.

Hakan na zuwa ne yayin da al'ummar Musulmi a ƙasashen duniya ke gudanar da azumin watan Ramadana, inda sukan ƙaurace wa ci da sha daga asuba har zuwa faɗuwar rana.

Wannan na nufin masu azumi ba za su iya shan ruwa ko wani abu da zai taimaka musu wajen kashe ƙishi ko yunwa ba.

To sai dai akwai shawarwari kan dabarun da mai azumi zai iya amfani da su domin rage hatsarin da zai iya faɗawa ciki sanadiyyar zafin yanayi.

Jihohin da yanayin zafin zai fi shafa a Najeriya su ne na arewa maso gabas, da arewa maso yamma da kuma arewa ta tsakiya:

Illar yanayin zafi ga lafiya

Bayanin na Hukumar kula da yanayi na Najeriya ya nuna cewa illolin da mutane za su iya fuskanta sanadiyyar yanayin zafin su ne:

  • Gajiya/Jiri
  • Rashin iya mayar da hankali
  • Rashin iya gudanar da aiki yadda ya kamata

Post a Comment

Previous Post Next Post