Rundunar ƴansandan Najeriya ta tabbatar wa BBC harin da ake zargin cewa mayaƙan Boko Haram ne suka kai hari a garin Ngoshe da ke jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar Borno, Nahum Daso Kenneth ne ya tabbatar da haka a ranar Juma'a, inda ya ce harin ya auku ne a daren ranar Laraba, amma bai tabbatar da adadin waɗanda aka kashe ko sace a harin."Lallai an kai hari, amma dai jami'an tsaro sun samu nasarar fatattakar maharan," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa jami'an tsaro na cigaba da ƙoƙarin ceto waɗanda ba a gani ba.
Kafofin yaɗa labarai a Najeriya ne suka ruwaito cewa an sace sama da mata da ƙananan yara 100 a harin, sannan kuma an ruwaito cewa maharan sun kashe jami'an sojin na Najeriya.
Jihar Borno ce cibiyar ayyukan mayaƙan Boko Haram da Iswap, ƙungiyoyin da suka sahfe sama da shekara 10 suna ƙaddamar da hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula a arewa maso gabashin Najeriya da kuma fadin yankin tafkin Chadi.
Duk da cewa a shekarun baya gwamnatin Najeriya ta yi ikirarin cin galaba a kan ƙungiyar, amma a baya-bayan nan ƙungiyar na ci gaba da ƙaddamar da hare-hare babu ƙaƙƙautawa kan jami'an tsaro da kuma fararen hula.
Wata sanarwa da jami'in yada labarai na rundunar Hadin Kai Laftanar Kamar Sani Uba ya fitar, ta ce rundunar ta yi nasara daƙile harin ƙungiyoyin masu dauke da makamai a garuruwan Gajiram da Gajigana da kuma Mayanti cikin kwana biyu kacan, wato tsakanin 28 ga watan Fabarairu zuwa 1 ga watan Maris.