Wani sabon rahoto daga cibiyar bincike ta Amurka Center for Strategic and International Studies (CSIS) ya bayyana cewa Amurka ta kashe kusan dala biliyan 3.7 a cikin awanni 100 na farko na hare-haren da take kai wa Iran. Rahoton ya nuna cewa fara irin wannan yaƙi na buƙatar kuɗi masu yawa saboda amfani da manyan makamai da fasahohin zamani.
Binciken ya nuna cewa wannan kuɗi ya kai kusan dala miliyan 891 a kowace rana. Masu binciken sun bayyana cewa farkon matakin yaƙin sama yawanci shi ne mafi tsada, domin ana amfani da makamai masu tsada kamar makamai masu linzami da sauran manyan kayan yaƙi.
Rahoton ya kuma nuna cewa yawancin kuɗin da aka kashe har yanzu ba su cikin kasafin kuɗin Ma’aikatar Tsaron Amurka ba. Saboda haka ana iya buƙatar gwamnati ta nemi ƙarin kuɗi daga majalisar dokokin ƙasar domin ci gaba da gudanar da yaƙin idan rikicin ya ci gaba.
Masu binciken sun ƙara da cewa sojojin Amurka sun riga sun yi amfani da fiye da makamai 2,000 a cikin awanni 100 na farko na yaƙin. Sake samar da waɗannan makamai kaɗai na iya kai kuɗin da ya haura dala biliyan 3.1.
Masana sun yi gargaɗi cewa idan yaƙin ya ci gaba na makonni masu zuwa, to yawan kuɗin da Amurka za ta kashe zai iya ƙaruwa sosai, wanda hakan zai iya jawo matsin tattalin arziƙi da na siyasa ga gwamnatin ƙasar.