Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Amnesty International ta ce gwamnatin Chadi ta gaza wajen kare fararan hula da rikicin makiyaya da manoma ke shafa a ƙasar.
A wani sabon rahoton da ta fitar, Amnesty ta ce ana cin zarafin fararan-hula da raba ɗaruruwa da matsugunansu, baya ga wadanda ake kashe wa da jikkatawa.Kungiyar ta ce a rikice rikice 7 da aka samu tsakanin makiyaya da manoma a larduna 4, waɗanda ake ganin matsalar sauyin yanayi ne ya ta'azzara samunsu, tsakanin shekarar 2022 zuwa 2024, alkalumanta sun nuna an kashe mutane 98 da jikkata sama da 100.
Rahoton ya kuma ce jami'an tsaro ba sa kawo ɗauki a kan lokaci, kuma ba a hukunta waɗanda ke kashewa da sacewa da kuma lalata dunkiyoyin alumma, wanda ke ƙara nuna danniya da zalunci tsakanin al'ummomi.