Kotun Najeriya Ta Yanke Wa Nnamdi Kanu Hukuncin Daurin Rai-da-Rai a Gidan Yari

 Kotun tarayya a Abuja ta yanke wa Nnamdi Kanu, jagoran ƙungiyar IPOB da aka haramta, hukuncin laifukan ta’addanci guda bakwai, tare da ɗaurin rai-da-rai.

Nnamdi Kanu

A hukuncin da Alƙali James Omotosho ya bayyana, kotu ta ce masu gabatar da ƙara sun gabatar da hujjoji masu ƙarfi cewa jawabai da umarnin da Kanu ke yi ta rediyo sun janyo ƙone-ƙone, hare-hare da kashe-kashe a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Daga cikin abubuwan da aka same shi da laifi akwai:

1. Tayar da zaune tsaye ta hanyar jawaban da suka hura wutar tashin hankali.

2. Umarnin "sit-at-home" da ya haddasa durƙushewar harkokin yau da kullum.

3. Jagorantar ƙungiyar IPOB, wadda gwamnati ta haramta a matsayin ƙungiyar masu tayar da zaune tsaye.

Masu gabatar da ƙara sun nemi hukuncin kisa, amma alƙali ya yi watsi da hakan, yana mai cewa kasashen duniya da dama ba sa goyon bayan hukuncin kisa, don haka ya zaɓi rai-da-rai.

Nnamdi Kanu dai ya ƙi amincewa da hukuncin, yana mai cewa shari’arsa ta dogara ne kan dokoki da aka soke tun daɗewa. Lauyoyinsa sun ɗaukaka ƙara suna neman Dakatar da hukuncin, tare da cewa an samu kura-kurai a tsarin shari’ar.

Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam kuma sun yi gargadin cewa wannan hukunci na iya ƙara hura wutar rikici a yankin da ke fama da matsalar kabilanci da ra’ayin ballewa tun shekaru.

Post a Comment

Previous Post Next Post