Tawagar Faransa Ta Yi Waje Da Daya-Dayar Tawagar Afirka (Morocco) Da Ta Rage A Gasar Cin Kofin Duniya

A ci gaba da fafatawa a gasar wasannin cin kofin duniya da yake gudana a ƙasashe 3 wato; Amurika da Canada da kuma Mexico. Jiya an sake karawa tsakanin Morocco da Faransa a Zagayen wasa na Quarter Final, Wanda suka kwashe mintina 60 cifcif ba tare da an samu wani wanda ya yi nasara a gasar ba. 
Sai dai tun bayan da mintinan 60 suka bayar da baya, tuni gwarzon ɗan wasan Faransa wanda yake taka leda a ƙungiyar Real Madrid Kulian Mbappe ya zura wata kyakkyawar ƙwallo a cikin raga mai ban sha'awa. Bayan mintina 4 da cin ƙwallon Mbappe shi ma Ousmane Dembele na ƙungiyar Paris ya zura tasa ƙwallon mai ban ƙaye, wanda haka suka riƙe wasan har zuwan mintinan tashi, ba tare da sun ƙara ci ko sun bari an ci su ba, Faransa 2 Morocco 0.
Wannan nasara da Faransa ta samu akan Morocco ita ce ta kawo ƙarshen wakilcin duka ƙasashe 10 na Afirka da suka shiga gasar cin kofin duniya a bana. Sai dai da yawan al'ummar Afirka ba su nuna damuwarsu a kan cire Moroccon ba, sakamakon batun da shugaban ƙasar Moroccon ya yi na cewa, "Morocco kanta take wakilta ba Afirka ba." Da alama wannan maganar ta yi wa 'yan Afirka zafi, wanda hakan ya sa wasu da yawa suka ji daɗin abin da ya faru da Morokon a daren jiya.

A shekarar 2022 wanda aka gudanar da gasar cin kofin duniya a ƙasar Qatar, idan ba ku manta ba, ƙasar Morocco ita ce ƙungiyar Afirka ƙwalli ɗaya da ta tsallake irin wannan matakin (Quarter Final) da aka koro su jiya zuwa matakin wasan kusa da na ƙarshe (Semi Final), ko iya haka lallai Morocco ta cancanci a kira ta da Zakanyar Afirka ko da kuwa shugaban ƙasarsu ba ya so, tun da dai ba zai iya cire ta daga Afirka ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post