Donal Trump Ya Yi Godiya Ga Hukumar FIFA Saboda Janye Jan Katin Dan Wasan Kasarsa

Fadar Shugaban Ƙasar Amurika (White House) wadda take ɗaya daga cikin ƙasashen da suka karɓi baƙuncin gasar cin kofin duniya, ta yi kira zuwa ga Hukumar Ƙwallon Ƙafa Ta Duniya (FIFA), inda ta roƙi shugaban ƙungiyar Gianni Infantino da a sake duba lamarin ladabtarwa na jan katin da aka bai wa ɗan wasan gaba na ƙasar ta Amurika Folarin Balogun a wasan da suka fafata da ƙasar Bosnia-Herzegovina, a mintina 64 da fara wasan. Lamarin ya faru ne bayan da alƙalin wasan ya amsa kira, domin ya je ya duba talabijin ta VAR domin kallon tsanaki na abin da ya faru. Bayan ya sake kallon yadda abin ya faru, sai ya tabbatarwa da masu kallo cewa lallai Balogun ya yi ƙeta wadda ta sa yanzu an ba shi jan kati.

A haka Amurka suka ci gaba da taka leda da mutane goma (10) har zuwa ƙarshen wasan, don ma sun riga da sun ci ƙwallaye 2 tun kafin lokacin.

To wannan laifin ne fa, Amurika ta ɗaukaka ƙara ga FIFA, wanda cikin sa'a kuma, ta karɓi ƙorafin, kuma ta tura shi kai tsaye zuwa ga kwamitin ladabtarwa.

Wasu majiyoyin' daga FIFA sun bayyana cewa, Fadar Shugaban ƙasar Amurika ba za ta iya sauya hukuncin da aka zartar ba, saboda ƙarfin ikon da yake ƙunshe a sashe na 27 na hukumar ƙwallon kafada kuma 'yancin cin gashin kan kwamitin ladabtarwa mai zaman kansa, ba tare da an yi masa kutse ba. Kwamitin shi ne yake da uwa makarɓiya akan duka hukunce-hukunce.

Bayan nazarin ƙwaƙwaf, daga ƙarshe dai FIFA ta soke Jan katin ɗan wasan na Amurika Balogun wanda zai taka leda a wasan da Amurika za ta fafata da Belgium a rukunin bugu ɗaya ƙwala na 'yan 16.

Bayan fitar da sanarwar janye hukuncin kan katin sai ga Shugaban Amurka, Donald Trump yana gode wa FIFA tare da bayyana cewa, "Ta yi abin da ya dace, kuma ta gyara babban rashin adalcin da aka yi.”

Post a Comment

Previous Post Next Post