An Kama Ɗan Najeriya da Katin Ecstasy 9,020 a Gambia

Hukumar Yaƙi da Safarar Miyagun Ƙwayoyi ta Gambia (DLEAG) ta kama wani ɗan Najeriya mai shekaru 53, Celestine Ikenna Godwin, da allunan ƙwayar ecstasy guda 9,020, da wasu adadin ƙwayar cannabis ruderalis, wadda aka fi sani da skunk, da kuma wata na’ura da ake zargin ana amfani da ita wajen ƙera da sarrafa miyagun ƙwayoyi.Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Dawda Sanyang, ya sanya wa hannu tare da wallafawa a shafin Facebook na hukumar ranar Juma’a.

A cewar hukumar, kama mutumin na wakiltar wata babbar nasara a yaƙin da take yi da safarar miyagun ƙwayoyi, musamman saboda gano na’urar da ake zargin ana amfani da ita wajen ƙera ƙwayoyi, wanda hukumar ta ce shi ne karon farko da ta samu irin wannan a Gambia.

Sanarwar ta ce an kama Celestine Ikenna Godwin da allunan ecstasy guda 9,020, tare da wasu adadin ƙwayar cannabis ruderalis da ake zargin skunk ce.

Hukumar ta ƙara da cewa an kuma kama shi da wata na’ura da ake zargin ana amfani da ita wajen ƙera da sarrafa miyagun ƙwayoyi.

DLEAG ta ce gano na’urar ya haifar da damuwa kan yiwuwar kafa dakunan ƙera miyagun ƙwayoyi na ɓoye domin samar da ƙwayoyin roba masu sa maye a cikin ƙasar.

Hukumar ta bayyana cewa gano wannan kayan aiki na da matuƙar muhimmanci, domin shi ne karo na farko da aka samu irin wannan lamari a tarihin ayyukanta a Gambia.

Ta ce lamarin ya ƙara haifar da babbar fargaba kan yiwuwar kafa dakunan ƙera miyagun ƙwayoyi a ɓoye a cikin ƙasar, tare da jaddada cewa barazanar safarar miyagun ƙwayoyi a yankin na ƙara sauya salo da kuma zama mai rikitarwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post