Ana Kada Kuri'ar Raba-Gardama Kan Kara wa Shugaban Guinea-Bissau Karfin Iko

Masu kada ƙuri'a a Guinea-Bissau za su kada ƙuri'ar raba gardama a yau a kan ko za a amince da wani sabon kundin tsarin mulki da zai ƙara wa shugaban ƙasar iko.

Ƙuri'ar ta zo ne ƙasa da wata goma bayan sojoji sun ƙwace mulki a ƙasar da ke yammacin Afirka.

An shirya gudanar da zaɓen gama gari a watan Disamba mai zuwa domin mayar da mulkin farar hula bayan juyin mulkin da aka yi a kasar.

Sai dai babbar jam'iyyar adawa ta ƙi shiga wannan ƙuri'ar raba gardaman.

Post a Comment

Previous Post Next Post