Kwakwalwa ce ta ke shigar da duk wani bayani dake tattare damu da wanda yake zagaye damu. Misali, aikin ƙwaƙwalwa ne ta rarrabe maka abubuwa, kamar sunan su, girman su, matsayin su, kalolin su, manufar su, darajarsu da duk wani abu dake tattare dasu.
Ita ce ke sanar da yanayi wanda ya hadar da sanyi, zafi ko matsakaici. Ita ke sanar da kai duk wani hali da kai kanka kake ciki. Itace ke gudanar da manyan ayyuka na cigaban rayuwar ka, kamar numfashi, isar da jini, isar da abinci, motsi, da sauransu.
Hasashen masana ya nuna cewa aduk daƙiƙa daya, ƙwaƙwalwa na tatsa da warwarar bayanai sama da miliyan daya. Daga cikin su ne ta ke rarrabe masu amfani da marasa amfani, sannan ta tsara yadda ya kamata a tafiyar dasu ba tare da ɓata lokaci ba duk a cikin mafi ƙanƙantar lokaci. Wannan gagarumin abin mamaki dake tattare da ƙwaƙwalwa ya sa shakku a zukatan waɗanda basu gamsu da wanzuwar Allah ba, domin tambayar su akayi da cewa "Ta yaya za a ce Na'urar kwamfuta wadda ba ta taka kara ta karya ba wajen abin mamaki idan aka haɗa ta da ƙwaƙwalwar dan adam za a ce wani ne ya yi ta, amma kuma ita ƙwaƙwalwar za a ce itace ta yi kanta?"
Kwakwalwar dan adam tana mafi karancin karfin ajiya daya kai Kimanin Gigabyte Miliyan biyu da rabi (2.5Million Gigabytes). Tabbas mafi karanci domin kuwa Kwakwalwar wasu, Allah ne kawai Masani.
