Ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Barista Mahdi Aliyu Gusau ta musanta rahotannin da ke iƙirarin cewa ɗan takarar gwamna na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ya janye daga takarar gwamnan Jihar Zamfara mai zuwa, tana mai bayyana rahotannin a matsayin ƙarya da yaudara.A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa yaɗa labarai kuma kakakin ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Barista Mahdi Aliyu Gusau, Abubakar Sulaiman, ya sanya wa hannu a ranar Lahadi, ƙungiyar ta ce Mahdi Gusau har yanzu shi ne ɗan takarar da aka amince da shi kuma sahihin ɗan takarar ADC a Jihar Zamfara.
Sanarwar ta jaddada cewa Mahdi Gusau bai janye daga takararsa ba, kuma bai yi watsi da burinsa na neman kujerar gwamnan jihar ba.
Ta bayyana rahotannin da ke yawo a matsayin aikin masu tayar da fitina, tare da buƙatar jama’a su yi watsi da su.
Ƙungiyar ta kuma sake tabbatar da cewa ɗan takarar na ci gaba da jajircewa wajen gabatar da manufofinsa na gina Zamfara mafi alheri ga masu zaɓe.
Haka kuma, ta shawarci jama’a da su riƙa dogaro da sanarwar hukuma daga ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Mahdi Aliyu Gusau domin samun sahihan bayanai game da halin da takararsa take ciki.