Shugaban Sojojin Sudan Al-Burhan Ya Yi Alkawarin Kariya Ga Masu Halartar Tattaunawa, Amma Ya Yi Watsi Da Komawar Hemedti

 Shugaban Majalisar Mulkin Sudan kuma kwamandan sojojin ƙasar, Abdel Fattah al-Burhan, ya yi alƙawarin samar da kariyar doka, siyasa da tsaro na wucin gadi ga mutanen da za su shiga wata tattaunawar ƙasa da nufin neman mafita ga rikicin Sudan.

Abdel Fattah al-Burhan

Al-Burhan ya ce za a dakatar da shari'o'in laifuka da ake yi wa mahalarta tattaunawar na wani lokaci yayin da suke cikin tsarin tattaunawar. Ya jaddada cewa wannan ba afuwa ba ce, illa dai dakatar da matakin shari'a na ɗan lokaci, ba tare da tauye haƙƙin waɗanda suka shigar da ƙorafi ba.

Ya kuma ce mahalarta za su samu damar bayyana ra'ayoyinsu da suka wajen tattaunawar ba tare da tsoron fuskantar gurfanarwa saboda abin da suka faɗa ba. Tsarin tattaunawar zai kasance ƙarƙashin wata ƙungiya mai zaman kanta, ba gwamnati ba.

Sai dai a batun yaƙin da ake yi tsakanin Sojojin Sudan (SAF) da Rapid Support Forces (RSF), al-Burhan ya ce ba zai amince da wata yarjejeniyar zaman lafiya da zai kira “zaman lafiya mara cika” wadda za ta mayar da Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, da magoya bayansa cikin mulki ba.

Ya ce duk wata hanya zuwa zaman lafiya dole ne ta fara da janyewar dakarun RSF daga birane da tattara su a wuraren da aka ware. Daga nan ne za a iya tattauna makomar mayaƙan RSF da yiwuwar haɗa waɗanda ba su aikata laifuka ba cikin rundunar sojojin ƙasa.

Wannan mataki na al-Burhan na zuwa ne yayin da ake ƙara ƙoƙarin farfaɗo da tattaunawar siyasa ta Sudan, bayan shawarwarin da ya yi da wasu 'yan siyasa da ƙungiyoyin farar hula a kwanakin baya.

Post a Comment

Previous Post Next Post