Sojoji sun kashe 'Yan Bindiga Biyu Tare da Kwato Makamai a Sokoto

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation FANSAN YAMMA sun kashe ƴan ta'adda biyu tare da kwato bindigogi da babura uku a wani samame da suka kai a ƙaramar hukumar Rabah da ke Jihar Sokoto

.

A cewar rundunar, samamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu a safiyar ranar 28 ga Agusta 2026 cewa wasu ƴan ta'adda na jan ɗaruruwan shanun da suka sace ta yankin Maikujera.

Daga nan ne sojojin suka yi gaggawar kai farmaki domin tare su.

Yayin da sojojin ke kan hanyarsu ta zuwa wurin, sun ci karo da kwanton ɓaunar da ƴan ta'addan suka yi musu.

Sai dai dakarun sun mayar da martani da ƙarfin wuta, inda anan ne suka kashe mutum biyu daga cikin maharan, yayin da sauran suka tsere zuwa cikin daji.

Rundunar ta ce shanun da aka sace sun watse cikin dazuka yayin fafatawar, amma ana ci gaba da haɗin gwiwa da ƴan sa-kai domin gano su.

Post a Comment

Previous Post Next Post