Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ’yan ta’adda 26 tare da dakile wani hari da aka shirya kai wa wani gari a jihar Borno.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da dare a kusa da ƙauyen Kadiya, da ke ƙaramar hukumar Kukawa, inda ’yan ta’addan suka yi arangama da dakarun Bataliyar Musamman ta 101 da misalin ƙarfe 10:45 na dare kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
Rahoton ya ce ’yan ta’addan sun ja da baya ne bayan da sojoji suka kai musu martani ta sama da ƙasa.
Daga nan ne Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kai hare-haren sama guda biyu kan ’yan ta’addan da ke ƙoƙarin tserewa.
An ce harin farko ya nufi kusan ’yan ta’adda 10 da suka fake a ƙarƙashin bishiyoyi, yayin da harin na biyu ya shafi waɗanda ke guduwa zuwa yankin Tunbuns/Kangarwa.
Rahoton ya ce hare-haren biyu sun kashe ’yan ta’adda 25 tare da lalata babura 10 da mayakan ke amfani da su.
A yayin wani aikin share fage da sojojin suka gudanar a safiyar Asabar kan hanyar da ’yan ta’addan suka bi wajen ja da baya, an gano gawar wani ɗan ta’adda guda, wanda ya ƙara adadin waɗanda aka kashe zuwa 26.
Sojojin sun kuma kwato harsasai 253 na 7.62 x 54mm PKT, harsasai 12 na musamman kirar 7.62mm da kuma harsasan kariya daga jiragen sama guda biyu.
