Yajin Aikin Ma’aikata ya Tilasta Enugu Air Sauya Jadawalin Wasu Jirage

Kamfanin jiragen sama na Enugu Air ya sanar da sauya jadawalin wasu daga cikin jiragensa sakamakon yajin aikin da ake yi a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Kamfanin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 11 ga Agustan 2026, inda ya ce an dakatar da ayyuka a filin jirgin na ɗan lokaci bayan ma’aikatan ƙungiyoyin kwadago sun hana jami’an filin shiga tashar jiragen sama.

A cewar kamfanin, wannan matsala na iya shafar wasu daga cikin jiragensa da ke zirga-zirga ta Abuja, yayin da yake ƙoƙarin daidaita tsarin tafiyarsa.

Sanarwar ta ce:

“Muna sanar da fasinjojinmu cewa, sakamakon yajin aikin da ake yi a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, inda ma’aikatan ƙungiyoyin kwadago ke hana jami’ai shiga tashar jirgin, an dakatar da ayyukan filin jirgin na ɗan lokaci.”

Kamfanin ya ƙara da cewa wasu daga cikin jiragensa na iya fuskantar sauyin jadawali har sai an sake sanarwa, yayin da ake ci gaba da gyara tsarin zirga-zirgarsa.

Enugu Air ya nemi afuwar fasinjojin da abin ya shafa, tare da tabbatar musu da cewa lafiyarsu da walwalarsu su ne abin da kamfanin ya fi bai wa muhimmanci.

Kamfanin ya shawarci fasinjoji da su rika duba saƙonnin imel, SMS da kuma shafukan sada zumuntarsa na hukuma domin samun sabbin bayanai kan matsayin jiragensu kafin su tafi filin jirgin sama.

Haka kuma, ya bukaci fasinjojin da ke buƙatar sake tsara tafiyarsu ko neman ƙarin bayani da su tuntubi sashen kula da kwastomomi na kamfanin.

NCAA ta roƙi ƙungiyoyin ma’aikata su dakatar da yajin aikin

Wannan ci gaba na zuwa ne yayin da rikicin masana’antu tsakanin ƙungiyoyin ma’aikatan harkar sufurin jiragen sama da kamfanonin jiragen sama ke ci gaba da haddasa tangarɗa ga zirga-zirgar jirage a faɗin ƙasar.

PUNCH Online ta ruwaito cewa Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA) ta roƙi ƙungiyoyin ma’aikatan da su dakatar da yajin aikin, tana mai cewa taron sasanta rikicin da Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama da Raya Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ya kira bai samu gudana ba saboda kamfanonin jiragen sama ba su halarta ba.

A cikin wata sanarwa da Darakta Janar na NCAA, Chris Najomo, ya sanya wa hannu a ranar Talata, hukumar ta bayyana cewa tana sane da tasirin da yajin aikin ke yi ga fasinjoji da sauran masu ruwa da tsaki.

Najomo ya yi kira ga ƙungiyoyin ma’aikatan da su kwantar da hankalinsu tare da nuna haƙuri har sai Minista Keyamo ya dawo domin ci gaba da ƙoƙarin warware rikicin.

Hukumar ta ce an tsara warware matsalolin a wani taro da ministan ya kira makon da ya gabata, amma taron bai gudana ba bayan da kamfanonin jiragen sama suka ƙi halarta.

Yajin aikin ya shafi Air Peace ma

Yajin aikin ya kuma shafi ayyukan Air Peace, mafi girman kamfanin jiragen sama na Nijeriya, bayan da ƙungiyoyin ma’aikata suka dakatar da ayyukansa a matsayin wani ɓangare na buƙatunsu.

NCAA ta sake yin kira ga dukkan ɓangarorin da su koma teburin tattaunawa domin warware rikicin.

Najomo ya ce:

“Muna roƙon dukkan ɓangarori da su rungumi tattaunawa da haɗin kai. Muna da tabbacin cewa za a warware matsalar cikin gaggawa kuma zirga-zirgar jirage za ta koma yadda take da zarar an samu mafita.”

Ya kuma tabbatar wa matafiya cewa yajin aikin bai taɓa lafiyar zirga-zirgar jiragen sama ba, domin NCAA na ci gaba da gudanar da aikinta na sa ido kan tsaron harkar sufurin jiragen sama.

Duk da haka, ya nemi afuwar fasinjoji kan matsalolin da suka fuskanta tare da roƙonsu da su ci gaba da nuna haƙuri yayin da ake ƙoƙarin sasanta rikicin.

A nata ɓangaren, Air Peace ta bayyana cewa tangarɗar da aka samu ta wucin gadi ce, kuma tana ci gaba da tuntuɓar fasinjojin da abin ya shafa domin ba su sabbin bayanai game da jadawalin jiragensu.

Enugu Air ita ma ta buƙaci fasinjoji da su ci gaba da bibiyar hanyoyin sadarwarta na hukuma tare da tuntubar sashen kula da kwastomomi domin sake tsara tafiya ko neman ƙarin bayani.

Post a Comment

Previous Post Next Post