Yayin da Amurka da Kanada ke ci gaba da taƙaddamar ciniki da juna, fargabar durƙushewar tattalin arziki na ƙara bayyana, yayin da masana da 'yan kasuwa ke nuna damuwa kan illar takunkuman ciniki da ƙarin haraji.
Rikicin cinikin na iya ƙara tsadar kayayyaki, rage harkokin kasuwanci da kuma yin illa ga kamfanoni da masu amfani a ƙasashen biyu.
Masana tattalin arziki sun yi gargadin cewa idan takaddamar ta ci gaba, za ta iya rage haɓakar tattalin arzikin ƙasashen biyu tare da ƙara yiwuwar samun koma bayan tattalin arziki.
A halin yanzu, 'yan kasuwa da masu zuba jari na sa ido sosai kan matakan da gwamnatocin Amurka da Kanada za su ɗauka, yayin da ake fargabar cewa tsawaita yakin cinikin na iya haifar da babbar illa ga tattalin arzikin Arewacin Amurka.