Wani sabon bincike ya gano cewa mutanen da ke aiki daga gida kuma suke zaune su kaɗai na iya kasancewa cikin haɗarin fuskantar kaɗaici da matsananciyar damuwa.
Binciken, wanda aka wallafa a mujallar Science, ya yi nazari kan bayanan bincike na ƙasa da aka tattara tsawon sama da shekaru 10.
Masu binciken sun gano cewa mutanen da ke zaune su kaɗai kuma suke cikin ayyukan da za a iya gudanarwa daga nesa, kamar tallace-tallace, suna shafe kusan kashi 25 cikin 100 na ranakunsu ba tare da hulɗar zamantakewa ba. Wannan ya ninka fiye da sau biyu idan aka kwatanta da mutanen da ke ayyukan da ke bukatar kasancewa a wurin aiki.
Haka kuma, binciken ya nuna cewa ƙaruwar matsalolin damuwa ta ƙwaƙwalwa tun bayan annobar COVID-19 ta fi yawa sau biyu tsakanin mutanen da ke zaune su kaɗai kuma suke cikin ayyukan da za a iya yi daga nesa.
Sai dai masu binciken sun jaddada cewa binciken bai tabbatar da cewa aiki daga gida shi ne ke haddasa matsalar lafiyar ƙwaƙwalwa ba.
Masana sun ce kasancewa a ofis ma ba ya nufin mutum zai samu kyakkyawar hulɗar zamantakewa. Sun ba da shawarar samar da shirye-shiryen jagoranci, ƙungiyoyin zamantakewa da sauran hanyoyin da za su taimaka wa ma’aikata wajen samun kyakkyawar hulɗa da sauran mutane.
Sun kuma ce ko da ƙananan mu'amala, kamar gaisawa ko ɗan taƙaitaccen hira da wani mutum, na iya taimakawa wajen rage kaɗaici da ƙara wa mutum jin cewa yana cikin al'umma.
