FADADA NOMAN KASUWANCI A KATSINA: Gwamna Radda Ya Amince Da Tallafin ₦361m Domin Waɗanda Suka Kammala Horon Songhai Su 361

Gwamna Radda ya amince da bayar da tallafin ₦361m ga waɗanda suka kammala horon Songhai su 361.

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya amince da bayar da tallafin fara sana'a domin tallafa wa matasa 361 'yan kasuwar noma waɗanda suka kammala horo a rukunin biyu na Tsarin Horo da Empowarment na 'Yan Kasuwar Noma na Dikko Radda (DRATESS-Songhai).

A ƙarƙashin wannan tsari, kowane ɗalibi zai sami tallafin naira miliyan ɗaya (₦1,000,000) domin gina sana'ar noma a cikin al'ummarsa.

Yayin da yake jawabi a wurin bikin yaye ɗaliban, Gwamna Radda ya jaddada cewa tsarin ya wuce batun samun takardar karatu kawai; ya fi maida hankali ne kan ƙwarewar aikace-aikace, dogaro da kai, da sake gina tattalin arziƙin jiha mai ɗorewa.

Gwamnan ya ƙara da cewa, "Noma ba kawai samar da abinci ba ne; kasuwanci ne, sana'a ce, dama ce ta zuba jari, kuma babbar hanyar sauya tattalin arziƙi ce."

Waɗanda suka ci gajiyar sun kammala zurfafa horo a fannoni daban-daban na harkar noma, wanda ya haɗa da noman amfanin gona da kiwon dabbobi da noman kifi da sarrafa kayan noma da amfani da hanyoyin makamashi da sake sarrafa shara, da gudanar da noman kasuwanci gabaɗaya.

Gwamna Ya Ƙwalafa Wa Waɗanda Suka Yaye Rai Kan Gina Sana'o'i, Maimakon Neman Aikin Gwamnati.

Gwamnan ya ƙarfafa wa sabbin waɗanda suka yaye gwiwa wajen rungumar tunanin kasuwanci, inda ya umarce su da su gina manyan kasuwanni da za su samar wa sauran mutane aikin yi maimakon jiran aikin gwamnati.

"Ina son in ga wasu daga cikin manyan 'yan kasuwa irin su Dangote sun fito daga Katsina," cewar Radda. "Kar ku ajiye takardun shaidar karatunku kuna jiran aikin gwamnati. Ku maida ƙwarewarku ta zama sana'o'i, sannan ku maida sana'o'inku su zama damammaki ga sauran mutane. Ku maida gona ta koma kasuwanci, kasuwanci ya koma masana'anta, masana'antu kuma su koma hanyoyin samun aikin yi ga mutanenmu."

Domin zurfafa tasirin wannan tsari, Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da shirin faɗaɗa Cibiyar Horo da Noma ta Makera Songhai da ke Dutsinma. Faɗaɗawar tana da nufin haɓaka ƙarfin cibiyar don ɗaukar 'yan kasuwar noma har 1,000 a kowane zaman horo.

Gwamna Radda ya ba da tabbacin cewa gwamnatin jiha za ta ci gaba da ba wa waɗanda suka cin gajiyar tallafi ta hanyar haɗa sana'o'insu da cibiyoyin kuɗi, 'yan kasuwa masu zaman kansu, kasuwannin kayayyaki, da shirye-shiryen ci gaba na ƙasa da ƙasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post