Rundunar ’yan sandan jihar Benue ta ce ta kuɓutar da mutane takwas daga cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su a kan hanyar Ankpenchi-Ogobia, a ƙaramar hukumar Ohimini ta jihar.Kwamishinan ’yan sandan jihar, Cletus Nwadiogbu, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar da ke Makurdi.
A cewarsa, wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun tare wata motar haya da misalin ƙarfe 11 na dare a ranar 13 ga Satumba, 2026, a kan hanyar Ankpenchi-Ogobia, inda suka yi garkuwa da fasinjoji 13.
Ya ce jami’an rundunar sun fara aikin ceto nan take, wanda ya kai ga kuɓutar da mutum huɗu, yayin da sauran mutane tara suka ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwar.
Kwamishinan ya bayyana cewa da misalin ƙarfe 6:30 na safiyar Juma’a, 18 ga Satumba, jami’an rundunar da ke aiki karkashin Violent Crime Response Unit, tare da sauran tawagogin yaƙi da miyagun laifuka, sun kai samame sansanin ƙungiyar masu garkuwar da ake zargi da aikata laifin, da ke yankin Ankpenchi na dajin Amla, a Ohimini.
Ya ce samamen ya haifar da musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da masu garkuwar, inda aka samu nasarar kuɓutar da mutum takwas daga cikin sauran waɗanda aka yi garkuwa da su.
Sai dai, ya ce abin takaici, ɗaya daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su ya mutu sakamakon munanan raunukan da masu garkuwar suka yi masa a lokacin harin. An ce gawarsa tana wani sashe na dajin.
Kwamishinan ’yan sandan ya ce mutanen da aka ceto suna cikin aminci kuma suna samun kulawar da ta dace.
Ya ƙara da cewa rundunar na ci gaba da ƙoƙarin cafke sauran mambobin ƙungiyar masu garkuwar da suka tsere, tare da gano gawar wanda ya rasu.
A wani labarin makamancin haka, a ranar Lahadi, rundunar ’yan sandan Najeriya ta ce ta kama mutane 262 da ake zargi da aikata laifuka tare da kuɓutar da mutane 27 da aka yi garkuwa da su a wasu samame daban-daban a sassan ƙasar.
Rundunar ta ce daga cikin laifukan da ake zargin waɗanda aka kama da aikatawa akwai garkuwa da mutane, fashi da makami, kisan kai, ’yan bindiga, ƙungiyoyin asiri, safarar mutane, fataucin miyagun ƙwayoyi, lalata kadarori da sauran laifuka.