Hare-haren da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a Colombia ke kaiwa da jiragen sama marasa matuƙa (drones) sun ƙaru da kashi 146 cikin 100 a cikin watanni biyar na farko na shekarar 2026, idan aka kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2025, a cewar Ofishin Kare Haƙƙin Jama'a na ƙasar.
Bayanan sun nuna cewa an samu hare-hare 121 tsakanin Janairu da Mayu 2026, inda aka kashe mutane 21, sannan aka jikkata 145, ciki har da yara. Fararen hula sun kai kusan kashi ɗaya bisa uku na mutanen da aka kashe ko jikkata. Hare-haren sun kuma lalata gidaje, makarantu, gidajen mai da wasu muhimman ababen more rayuwa.
Ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai na amfani da drones wajen kai hare-hare kan sojojin gwamnati da ƙungiyoyin abokan hamayya, sannan kuma wajen sa ido a wuraren da ake noman coca ba bisa ƙa'ida ba. Wasu daga cikin drones ɗin ana ɗora musu abubuwan fashewa, lamarin da ya ƙara barazana ga fararen hula da jami'an tsaro.
Ofishin Mai Kare Hakkin Jama'a ya ce tsoron hare-haren drones ya sa wasu al'ummomi suka kaurace wa gidajensu, tare da fuskantar matsalolin zirga-zirga, zuwa asibitoci da gudanar da ayyukan yau da kullum. Gwamnatin Colombia ma ta sanar da wani shiri na dala biliyan 1.68 domin samar da tsarin kariya daga drones.
Masu sa ido sun ce yawaitar amfani da drones na nuna wani sabon salo a rikicin makamai na Colombia, musamman a yankunan da ke fama da rikice-rikicen ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da harkokin safarar miyagun ƙwayoyi.