Hukumomi a jihar Neja sun ƙaƙaba dokar hana fita a Minna, babban birnin jihar Neja sakamakon zanga-zangar da ta ɓarke.
Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan yaɗa labarai, Zayyanu A Salihu ya wallafa sanarwar a shafinsa na Instagram.
Ya ce dokar ta tsawon sa'a 24 za ta soma aiki bayan sallar Juma'a.
Hukumomi sun shawarci jama'a da su mutunta dokar.
Wani mazaunin Unguwar Tunga Sabon Titi inda lamarin ya faru, wanda kuma ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC cewa matasan da suka fusata sun yi ta jefe-jefe yayin da ƴansanda kuma ke harbi.
A cewarsa, ƴansanda sun harbi mutum huɗu kuma a cikinsu mutum guda ya mutu nan take.
Da farko, jami'ai sun yi zargin cewa wata cuta ce ta yi sanadin mutuwar matasa da ake zargi da haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba.
Tuni dai gwamnatin jihar ta Neja ta sanar da kafa kwamitin bincike don gano musabbabin mutuwar matasan