Tsohon shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya), ya ce ba za a iya kawo karshen ta’addanci da tayar da kayar baya ta hanyar amfani da karfin soja kadai ba.
Buratai ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da littafin “Military Transformational Leadership in Action: The Buratai Era”, wanda M.S. Abubakar ya rubuta, a Abuja.
Ya ce nasarar yaki da ta’addanci na bukatar hadin gwiwar hukumomin gwamnati, al’umma, sarakunan gargajiya da shugabannin addini, da kuma abokan hulda na kasa da kasa.
Buratai, wanda ya rike mukamin Shugaban Sojoji daga 2015 zuwa 2021, ya ce a lokacin da ya karbi ragamar rundunar, Boko Haram na rike da wasu yankuna, lamarin da ya tilasta wa jama’a barin gidajensu tare da rage musu kwarin gwiwa kan tsaro.
Ya ce gwamnatinsa ta aiwatar da sauye-sauye da kafa sabbin rundunoni domin kara karfin aikin sojoji, tare da inganta walwala da kwarewar jami’an.
Marubucin littafin, Abubakar, ya ce ya fara tattara bayanai kan zamanin Buratai tun 2016, inda ya kwashe kusan shekaru 10 yana bincike kan sauye-sauye da ayyukan yaki da tada kayar baya a lokacin.
Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya yaba da salon jagorancin Buratai, yana mai cewa tsohon shugaban sojin ya taimaka wajen gano tare da bunkasa jami’an da daga bisani suka zama manyan kwamandojin rundunar.
