Majalisar Zartarwa ta Jihar Katsina, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umaru Radda Ph.D, ta gudanar da taro na 16 a shekarar 2026, inda a taron aka amince da wasu muhimman shirye-shirye da suka shafi mata, musamman akan ababen more rayuwa da ilimi.
Majalisar ta amince da wani gagarumin shirin tallafa wa mata 49,640 a mazaɓu 361 na ƙananan hukumomi 34 na jihar, musamman mata masu ƙananan sana’o’i da ’yan kasuwa.
Haka nan, majalisar ta amince da bayar da kwangilar sake gina hanyar Bindawa da Dallaje da Doro da Giremawa da Duwan da Kwanar Duwan, wadda ake sa ran za ta sauƙaƙa zirga-zirga tare da haɗa al’ummomin yankin da kasuwanni da asibitoci da makarantu.
Majalisar ta kuma amince da rahoton kwamitin da aka kafa domin shirin tallafin karatu ga mahaddatan Alƙur’ani a faɗin jihar, domin ba su damar ci gaba da karatu a fannoni daban-daban.